5 Agusta 2021 - 11:47
​ Iran : Manya-Manyan Baki Sun Fara Isa Tehran Don Halattar Bikin Rantsar Da Shugaba Sayyid Ibrahim Ra’isi

Manyan baki daga kasashen duniya daban-dabn sun fara isa birnin Tehran don halattar bikin rantsar sabon shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jalil Rahimi Jahan-abadi mamba a kwamitin al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a safiyar yau Laraba.

Jahan-Abadi ya kara dacewa da shi da wasu jami’an gwamnatin kasar sun yi maraba da kakakin majalisun dokoki na kasashen Uzbekistan, Tajakistan da kuma Niger tare da tawagoginsu a safiyar yau Laraba. Har’ila yau labarin ya kara da cewa tawagar ‘yan majalisar dokokin kasar Guinea Conakry ta isa tashar jiragen sama na Imam Khumaini (q) da ke nan Tehran a safiyar yau Laraba.

Sauran bakin da suka karasu nan Tehran sun hada da Kakakin majalisar dokokin kasar Zanzibar da na Tanzania, har’ila yau tawagar diblomasiyyar Vatican ta isa Tehran a safiyar yau Laraba.

Ministan harkokin wajen kasar Bangladesh mataimakin ministan harkokin wajen kasar Korea ta kudu duk sun isa birnin Tehran. Sannan shugaban majalisar dattawan kasar Pakistan zai isa birnin Mashad daga arewacin kasar kafin ya karasa Tehran a gobe Alhamis.

Da misalign karfe 5 na yamma agogon Tehran ne ake saran za’a rantsar shugaba Ibrahim Ra’isi a matsayin shugaban kasar Iran na 13 tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar.

342/